Mark 8

1A kwanakin nan, akwai wani gagaruman taron mutane, kuma basu da abincin ci. Yesu ya kirawo almajiransa yace masu, 2“Ina tausayin taron mutanen nan domin kwana uku kenan suna nan tare da ni babu abinci. 3Idan na salame su su koma gidajensu ba tare da sun ci abinci ba, za su galabaita a hanya domin gidajensu na da nisa.” 4Almajiransa suka amsa masa cewa, “A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?”

5Ya tambaye su, “gurasa nawa kuke da su?” Sai suka ce, “Bakwai.” 6Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa’annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu.

7Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen. 8Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai. 9Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su. 10Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta.

11Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi. 12Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, “Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar.” 13Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin.

14A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan. 15Ya gargade su, “ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus.”

16Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, “Saboda ba mu da gurasa ne.” 17Yesu yana sane da wannan, sa’annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?”

18Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba? 19Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, “Goma sha biyu.”

20Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, “bakwai.” 21Ya ce masu, “har yanzu baku gane ba?”

22Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi. 23Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi “kana ganin wani abu kuwa?”

24Ya daga ido sai ya ce, “ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa.” 25Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau. 26Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, “kada ka shiga cikin garin”

27Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, “Shin wanene mutane ke ce da ni?” 28Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, “Iliya”. wadansu kuma, ‘Daya daga cikin anabawa”.

29Ya tambaye su, “Amma me ku ke ce da ni?” Bitrus ya ce, “Kai ne Almasihu.” 30Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi.

31Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu. 32Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa.

33Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa’annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, “Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba.” 34Sai ya kira taron jama’ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, “Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni.

35Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi. 36Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa. 37Me mutum zai bayar amaimakon ransa?

Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki.”

38

Copyright information for HauULB